1

Na farko: Ya wajaba ga mai yin Addu’a da tsarkake Addu’arsa ga Allah SWT, kuma ya sanin na tabbaci cewa Allah SWT ne shi kaxai mai iko kan amsa masa Addu’arsa, kada ya roqi wanin Allah ko yayi Tawassuli dad a waninsa, ko kuwa yaya yake kuma koda Annabi ne ko Malaika ko wani Bawa nagari koma yaya yake saboda faxin Allah maxaukakin Sarki: “Saboda haka ka roqi Allah kana Mai tsarkake Addini a gare shi” [Surat Gafir: 14].

1/16