﴿اللَّهُمَّ مَالِكَ الْمُلْكِ تُؤْتِي الْمُلْكَ مَن تَشَاءُ وَتَنزِعُ الْمُلْكَ مِمَّنْ تَشَاءُ وَتُعِزُّ مَن تَشَاءُ وَتُذِلُّ مَن تَشَاءُ بِيَدِكَ الْخَيْرُ إِنَّكَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ ٢٦ تُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَتُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ وَتُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَتُخْرِجُ الَمَيِّتَ مِنَ الْحَيِّ وَتَرْزُقُ مَن تَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَاب﴾
{آيتان من سورة آل عمران آية (٢٦-٢٧)، وفي أول الآية الأولى حُذفت كلمة (قل) عمدًا للإشارة إلى بداية الدعاء.}
(Allahumma maalikal mulki tu’util mulka man tashaa’u wa tanzi’ul mulka min man tashaa’u wa tuzillu man tshaa’u wa tu’izzu man tashaa’u wa tuzillu man tsha’u biyadikal khairi innaka alaa kulli shai’in qadiirun)Tuulijul laila fin nahari wa tuulijunnahara fillaili wa tukhrijul hayya munal mayyiti wa tukhrijul mayyita minal hayyi wa tarzuqu man tasha’u bigairi hisaabi)
Ka ce:* "Yã Allah Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne.
"Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba."
Ayoyi biyu daga cikin Surat Ali Imran Aya ta 26, da 27 a farkon Ayar farko an shafe Kalmar (Ka ce) da gangan don nuni da farkon fara Addu’a.