12

* Akwai Wasu Sharaxai da kuma wata Nusarwa wacce ya kamata a kula da ita a cikin Ruqya su ne:

1. Ta kasance Ruqya ce ingantacciya daga littafin Allah da Sunna, wacce take nesa ga barin Shirka da Bidi’a da Haramun duk xaya ne ai a Hanyarta ko lafazanta.

2. Lallai cewaMusulmi ya xanfara da Ubangijinsa kuma ya dogara das hi, kuma ya sani cewa lallai Euqya Sababi ce bata da wani Tasiri said a yardar Allah Maxaukaki.

3. Kada ya zo da Ruqya sai ta Hanyar gwaji, aa ya Wajaba ya yi Imani da Tasiriinta, saboda cewa Mai Ruqya da wanda akewa Ruqya tana da tasirim Ruqya din da warkewarsa

4. Al-qurani Mai girma dukkan Ayoyinsa Waraka ne, Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma muna saukar da Wannan Al-qur’ani abunda yake waraka kuma Rahama ce ga Muminai” sai dai Ruqya da abunda ya zo a Nassi it ace ta fi.

5. Abun da ya fig a Mara lafiya yayi wa kansa Ruqya da kansa, saboda wannan shi ne mafi anfani a gare shi kuma mafi yawan gasgatawa wajen bayyana buqatar sa saboda halarto da Zuciya da tsarkake Niyya gare shi yana da Tasiri a wajen Ruqya.

12/12