8

Ya Voye Addu’arsa kuma kada ya bayyana ta, saboda faxin Allah SWT: “Ku roqi Ubangijinku kuna masu qanqan da kanku da kuma voyewa” [Al-a’araf: 55], da kuma voye Addu’a shi ne mafi kusanci da ikhlasi, saboda yabon da Allah yayiwa Annabi Zakariyya –Amincin Allah a gare shi- da wannan sai y ace: “Ka tuna lokacin da ya roqi ubangijinsa roqo a voye” [Maryam: 3] saboda neman Ikhlasi, kan daidai da xaya daga cikin Maganganun Malaman tafsiri.

8/10