6
Ya roqi Allah SWT da sunayensa Masu tsarki kuma ya riqa nau’antawa da abunda ya d ace da Addu’a, idan zai roqi Allah SWT Arziqi, y ace: Ya Mai Azurtawa, Kuma idan zai roqi Allah Rahama, sai y ace Ya rahman ya Rahim, kuma idan zai roqi Allah Xaukaka y ace: y ace Ya Azizu, kuma idan zai roqi Allah gafara, y ace: ya Gafour, kuma idan zaka roqi Allah da Waraka, sai y ace: Ya Shafi, kuma haka dai zai rinqa Addu’a ya kirawo sunan day a dace da Addu’arsa, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma ga Allah kyawawan Sunaye suke saboda haka ku roqe shi dasu” [A’araf: 180]