5
Lallai cewa ya roqi Allah kuma yana mai kyautata zato das hi, kuma ya sakankance da Amsar Addu’a kuma kada ya gaggauta neman Amsawa, a’a ya sakankance cewa Allah yana Amsa Addu’arsa, An rawaito daga Abu Huraira daga manzon Allah SAW y ace: “Ba’a gushe ba ana Amsa Addu’ar Bawa matuqar dai bai roqi Zunubi ba ko yanke zumunci, ko kuma yayi gaggawar” aka ce ya Manzon Allah yaya ne gaggautawar? Ya ce: “Haqiqa nayi Addu’ar, banga Amsar hakan ba sai ya xebe haso ya bar Addu’ar daga nan”