4

Ya fara a cikin Addu’arsa da kirari ga Allah _-Maxaukakin Sarki- da kuma Salati ga Manzon Allah SAW saboda Hadisin da aka rawaito daga Fudhala Bn Ubaid Sahabin Manzon Allah SAW yak e cewa naji Manzon Allah SAW yana cewa wani Mutum da yayi Addu’a a sallarsa bai yi kirari ga Allah ba, kuma bai yi Salati ga Manzon Allah SAW ba Sai Manzon Allah SAW y ace: “Wannan yayi gaggawa” sanna ya kirawo shi y ace das hi: “Idan xayanku yayi sallah to ya farad a kirari ga Allah da yabo a gare shi, sannan yayi Salati ga manzon Allah sannan yayi Addu’a bayan haka da abunda yak e so” Kuma da za’a ce ya farad a Yabon Allah Musammam AYoyin yabon Musamman Ayoyin godiya waxanda suka zo daga a farkon Surorin da zamu faxa a gaba, sannan yayi salati ga Manzon Allah SAW sannan yayi kirari ga Allah da nau’o’in Kirari daga cikin su akwai waxan da zamu faxa nan gaba to ya kasance mafi kusa da samun Amsawa.

4/10