10

Mai Addu’a ya kirdadi lokacin Amsar Addu’a sai yai Addu’a a cikinta. Kuma daga cikin lokutan amsar Addu’a waxanda suka zo a cikin Qur’ani da Hadisi: (Addu’a tsakanin kiran Sallah da Iqama – da cikin kaso xaya na ukan Qarshen dare – da kuma cikin lokacin Sa’ar jumu’a da bayan Sallolin Farilla da cikin Sujada da lokacin saukar rowan Sama da Addu’ar Musulmi ga Xan Uwansa a voye, da Addu’ar Uba da Xansa, da Addu’ar da Addu’ar Matafiyi, da Addu’ar wanda aka zalunta).

10/10