1
Yayi Addu’a cikin tsarki kuma yayi Alwala irin Alwalar Sallah; saboda hadisin Abu Musa –Allah ya yarda das hi- wanda yak e cikin Buhari da Muslim, kuma wanda ya qunshi Qissarsa da Baffansa Abu Amir –Allah ya yarda da shi- kuma a cikin Hadisin Abu Amir yayi wa Abu Musa wasiyyar day a nemi Manzon Allah SAW yayi Masa Addu’a sai Abu Musa ya bashi labari, sai Manzon Allah ya nemi akawo Masa Ruwa sai yayi Alwala sannan ya xaga Hannayensa, sannan y ace: “Ya Ubangiji ka gafartawa Ubaid, Abu Amir” har said a naga farin Hammatarsa, sannan y ace: “Ya Ubangiji ka sanya shi a Ranar Alqiyama sama da mafi yawan Halittunka na Mutane” .