Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, kuma tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa mai girma, da Alayansa da Sahabbansa baki xaya, wannan wani xan qaamin littafi ne wanda a cikin sa akwai Addu’o’I daban daban da suka tare dukkan Addu’o’I, (Yabo ga Allah da kuma Addu’o’in Qur’ani).
Da kuma Addu’o’in Annabi SAW, da Addu’o’in neman tsari na Manzon Allah SAW da Ruqya ta Shari’a da zikirorin Safiy da Maraice) da kuma ladaban Addu’a , kuma na yi kwaxayin zavo ingatattun Addu’o’I daga Qur’ani da Sunnar Manzon Allah waxanda suka tattare dukkan Alkairai Masu Yawa, kuma na rubuta shi da Yaren larabci kuma aka fassara shi da Yaren (HAUSA) da kuma rubuta yadda ake furta wannan Addu’a, kuma na faxi Ingancin Hadisan Addu’o’in a qarshen littafin, kuma ina roqon Allah SWT day a sanya wannan aikin sadoda shi akayi kaxai, kuma Allah kayi Sati da tsira ga Annabinmu Muhammad da Alayansa da Sahabbansa baki xaya.
Dr. Abdullah Bn Hamud Al-furaih